Fira ministan HKI Benjamin na tanyaho ya sanar cewa ba zai taba janye sojoji daga yankunan da suka mamaye yanzu haka ba a yankin Gaza, kana kuma yayi watsi da shirin zaman lafiya na kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya da kuma kwance damarar kungiyar Hamas , kamar yadda kafafan yada labaran isra’ila suka nakalto, cewa kun aiko mana da sabon shiri, bamu amince da shi ba domin ba tsarinmu ba ne kuma mun aika muku da mahangarmu akai
A makon nan ne kungiyar Hamas ta sanar da kudurinta na ci gaba da gwagwarmya dama dukkan kungiyoyin yan gwagwarmaya kan abin da aka cimma matsaya akai, game da batun fara aiki da mataki na biyu na yarjejeniyar dakatar da Bude wuta da aka cimma tsakaninsu da Isra’ila a watan oktoban shekara ta 2025, sai dai duk da haka isra’ila ta ci gaba da kai hari a kokarinta na rusa yarjejeniyar
kuma wannan yana zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila take ci gaba da ketara yarjejeniyar dakatar da bude wuta da kuma ci gaba da kisan kare dangi kan alummar Gaza , musamman ma hare-haren da takai mafi muni a yan kwanakin da suka gabata