Miliyoyin mutane a kasar Iran daga ciki har da mutanen Tehran ne suka fito kan tituna daga dandalin Imam Hussain (a) da ke tsakiyar birnin zuwa Haramin Abdul azim alhasani da ke tazarar kilomita 14 daga tsakiyar birnin wato garin Rai da kudancin birnin Tehran.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya bayyana cewa ana kiran wadanda basu sami damar zuwa hubbaren Imam Al-Hussain (a) da ke birnin Karbala na kasar Iraki don gudanar da makokin 40 nasa ba, a matsayin wadanda aka barsu a baya.
A tattakin 40 na bana dai, wanda ya zo cikin yanayin yaki a kasar mutane da dama suna dauke da jajayen tutoci wanda yake nuna alamar daukar fansa kan kisan jagoran juyin juya halin musulunci kasar Imam Sayyid Aliyul Khaminaei (q) wanda Amurka da HKI suka yi a farkon yakin da ake fafatawa a kuma farkon wannan shekarar.
An gudanar da irin wannan tattakin a duk manya da kananan garuruwa a kasar, kuma a nan Tehran Jami’an gwamnatin kasar sun bayyana cewa sun samar da motocin bus bus wadanda zasu yi jigilar mutane har 800 zuwa anguwanninsu, sannan akwai wuraren rarraba abinci da abinsha a kan hanya har guda 3,500.