Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanar da karin albashi mai tsoka ga dakarun kasar domin karfafa wa sojojin gwuiwar samar da tsaro da kuma fatattakar ƴan ta’addan da suka hana zaman lafiya a cikin kasar.
A karkashin sabon tsarin da Bayo Onanuga ya raba wa manema labarai, an kara wa sojoji masu mukamin kurtu zuwa Staf Sajent kashi 80 na albashinsu, yayin da kuma masu mukamin Kanar zuwa Waran Ofisa suka samu karin kashi 50 na albashin da suke dauka yanzu haka.
Sanarwar ta ce daga masu mukamin Birgediya Janar zuwa Janar kuma, za su samu karin kashi 30 daga albashin da suke dauka yanzu haka.
Wannan adadi, kamar yadda Onanuga ya bayyana, zai sanya albashin sojojin dake sadaukar da ransu wajen kare ƴan Najeriya ya tashi daga naira biliyan 660 kowacce shekara zuwa naira biliyan 924.
Kakakin shugaban kasar ya ce Tinubu na alfahari da kuma jinjina wa sojojin saboda kwazon da suke nuna wa wajen sadaukar da rayukansu wajen tinkarar ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane da kuma ayyukan ta’addanci a faɗin Najeriya.
Tinubu ya ce ya zama wajibi a goya wa masu kare lafiyar ƴan Najeriya baya da kuma mutunta ayyukan da suke yi na tsaron ƙasa.kuma ya buƙaci sojojin da su yi amfani da wannan ƙarin wajen daɗa jajircewa domin tabbatar da tsaron Najeriya.