Rahotannai sun bayyana cewa dakarun sojin kasar Yamen sun kaddamar da harin da jirgin sama mara matuki a filin hawa da saukar jiragen sama na Najran dake kasar Saudi Arbeiya, kuma wannan hari mayar da martani ne kan hare-haren da gwamnatin riyad din take kai wa kasar yamen
Birgediya Janar yahya Saree kakakin sojin kasar Yamen yace dakarun sojin kasar sun kai hare kan wani wuri mai muhimmanci a kasar Saudiya da jirgin sama mara matuki da aka yi a cikin gida, kuma hari martani ne kan keta hurumin kasar da saudiya ke yi a larduna dake arewacin sa’ada da Hajja a kasar yamen
Yace mun gargadi kasar saudiya cewa duk wani hari da za ta kai to ba zai tafi hakan nan ba ba tare da mayar da martani ko daukar fansa ba, a ranar 20 ga watan yuli ne gwamnatin sana’a ta sanar da sanyawa kasar saudiya takunkumi kan jiragen ruwanta , saboda takunkumin zalunci da saudiya ta sanya mata na tsawon shekaru 12
kasar saudiya da sauran kawayenta na kasashen larabawa sun sanya takunkumi kan kasar Yamen a wani bangaren na shelanta yaki tun a watan maris din shekara ta 2015 ta hanyar amfani da taimakon da take samu na siyasa, Soji da sauran kayan aiki daga Amurka da sauran kasashen yammcin turai