Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 212

212-Assalamu alikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmi na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka

212-Assalamu alikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmi na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

////…Madallah, Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma sirar Imam Al-Hassan Al-Mujtaba (s) dan Fatimah (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo mako, a cikin shirimmu da ya gabata mun ci gaba da kawo maku martanin da Imam Al-Hassan (a) yake yiwa mutanen Mu’awiya bayan sun kirashi suka aibata shi da shi da Mahaifinsa Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib (a), duk a cikin ziyarar da ya kai kasar Sham.

Muka ce da farko ya bayyana masu cewa Mu’awiya ne ya zage shi, da kuma mahaifinsa (a), don haka sai ya fara da shi, ya kuma bayyana aibobinsa da laifukansa har ya kaiga mu’awiya ya yi nadamar hada taron gaba daya. Sannan ya fara da Amru dan Asi daga cikin mutanen mu’awiya wadanda suka yi masa rashin kunya da shi da mahaifinsa Imam Ali (a).

Ya bayyana yadda mahaifiyarsa ta Haifeshi, da kuma yanda aka zami Asi ya zama babansa. Ya bayyana yanda yake adawa da musulunci da manzon All..(s) a farkon bayyanar sa, da kuma yanda suka shiga musulunci, amma ba abinda ya sauya a halayensu. Sannan yanda suka dirar mikiya a kan iyalan manzon All..(s) bayan wafatinsa. Wanda ya kara tabbatar da cewa, basu amfana da addinin musulunci ba in banda don kyautata duniyarsu.

Sun yaki wasiyan manzon All..(s) sun kwace iko daga hannunsu, sun sauya al-amura da dama a musulunci bayan sun sami iko a kan musulmi.

Zamu tashi daga inda Imam Al-Hassan (a) ya juya kan Walid dan Ukba  yana cewa:

{.. Amma ya kai walidu, na rantse da All.. bana aibataka saboda kiyayyarka ga Aliyu (a), saboda ya yi maka bulala 80 haddin shan giya, ya kuma kashe babanka a gaban manzon All..(s) (a ranar badar), kuma All..ya kiraka fasiki ya kira Aliyu Muminin, a lokacinda kuka yi nuna fifiko da alfakhari a tsakaninku, a lokacinda kace masa, ka yi shiru ya Ali(a), Lalle mu mun fika daukaka da jarunta, kuma mun fika iya magana, sai Aliyu (a) yace maka: Ka yi shiru ya Walidu, ni muminine kai kuma fasiki, sai All..ya saukar da Aya. Wacce ta yi dai dai da abinda ya fada maka, yana cewa {Shin wanda ya kasance mumini dai dai yake da fasiki? Ba zasu zama dai daivb! }

Sannan ya sake saukar da wata aya wacce ta yi dai dai da abinda ya fada maka, yana cewa {Idan fasiki ya zo maku da labara ku yi bincike}. Kaitonka ya Walid ! Ko ka manta ba zaka manta wata kisidar da wani ya tsara kanka (sai ya kawo kasidar tana cewa).

Na Rantse da All..wanda ya kasance Mumini. Ba zai zama dai dai da Fasiki ma’kha’inci ba.

Da sannu nan gaba kasan za’a kira Al-Walidu. A kuma kira Ali Zuwa ga Hisabi Da kansu.

A sakawa Aliyu saboda haka da Aljanna. Sannan a sakawa Walidu yana kaskantacce.

Sai yace: Me ya hadaka da Quraishawa ma, ya kai wali du, kai ba kome ba sai mutum daga mutanen safuriyya, (wani wuri a kusa da kasar Jordan). Kuma shekarunka ya fi yanda ake daukanka.

Sannan ya jiya kan Utbatu dan Abusufyan (dan’uwan mu’awiya) yana cewa: {Kai kuma ya Utbah ! kai ba mai kaifin hankali ne ba, da sai in baka amsa, baka da hankalin fahinta da zai yi muhawara da kai ba ko in aibata ka ba, ku ba wani alkhairi tattare da kai wanda wani zai yi kaunar samunsa daga wajenka, kuma kai ba zaka iya cutar da ni ba, sai a ji tsoron cutawarka, hankalinka da na kuyangarka daya ne, me Aliyu (a) zai cutu da kai, idan ka zage shi a gaban jama’a, amma barazanar kashe ni da kayi ! inda zaka iya da ka kashe Al-lahya a lokacinda ka sameshi da matarka mana, shin baka kunyar zancen Nasru dan Hajjaju dangane da kai, kan wannan al-amarin  ba? Bayan wannan, ina jin kunyar in kawo kalmomin alfasha da ya kawo, kuma ta yaya wani zai ji tsoron takobinka, al-hali ka kasa kashe wanda ya kunyataka a kan gadonka. Sannan ba zan zargeka da kin Aliyu (a) ba, saboda ya kashe kawunka Walidu a mubaraza ta dai daiku a ranar yakin badar?, sannan ya yi tarayyar da Hamza wajen kashe kakanka Utbah, sannan ya rabaka da dan’uwanka Hanzalah a lokaci guda?.}.

Sai Imam Al-Hassan (a) ya juya wajen Mughira dan Shuba yana ce masa

{Amma kai Mughira! Baka cancanci shiga cikin wannan al-amari da ka sa kanka da makamancinsa ba, don kwatankwacinka kamar sauro ne ya fadawa kudan zuma (ki tsaya da kyau don zan tashi! Sai kudan zuma ta fada mata cewa, ina na san ka sauka a kai na, ballanta na in san zaka tashi?) . Na Rantse da All..bama dan kana adawa da mu ba, kuma ba zamu yi bakin ciki ba, idan ma mun san kana adawa da mu ba. Zancenka a kammu baya da damummu, kuma ka san cewa haddin zina ya tabbata a kanka, Hakiki Umur ya dauke maka hakkin All.. kuma All..zai tambaye shi kan hakan . Kuma ka tuna, ka taba tambayar manzon All..(s) kan cewa: Ya halatta ga namiji ya kalli mace wacce yake son aurenta? Sai Yace maka: Babu laifi ya Mughira, matukar baya nufin zina don ya san kai mazinaci ne. Amma alfakharin da kake mana da samun shugabanci! All..yana cewa:

 {Kuma Idan mun yi niyyar halaka wata Alkarya, sai mu shugabantar da mabarnatansu, su yi barna a cikinta, sai zance ta tabbata a kanta, sai mu diketa nikewa} Isra 16  }.

Wannan kadan Kenan daga cikin muhawarorin Imam Al-Hassan (a) da mu’awiya da mutanensa a ziyarar da ya kai kasar sham a lokacin Khalifancin Mu’awiya dan Abu sufyan.

Malaman tarihi sun bayyana cewa, a lokacinda Imam Al-Hassan (a) ya lallasasu, ya bayyana laifukansu, sai ya juya zai tafi, sai Amru dan Asi ya zo ya kama gefen rigarsa yana cewa:

Ya Amirul muminina ! (yana nufin Mu’awiya dan Abusufyan) hakika ka ji zancensa na kazafi ga mahaifiyata, ina mai neman a hukuntashi da laifin kazafi ga mahaifiyata.

Sai Mu’awiya ya tsawata masa, cikin fushi yana cewa: Ka sake shi! Kada All..ya saka maka da Alkhairi! Sannan ya juya kan mutanensa, wadanda suka fara aibata Imam Al-Hassan da mahaifinsa yana cewa.

‘Na fada maku, shi mutum ne wand aba za’a iya jayayya da shi ba, na hana ku zaginsa, kuka saba mani. Kuma na Rantse da All.. bai tashi ba sai da ya bakanta mani gida. Ku tashi ku tafi All..ya kunyataku, ya tabar da ku. Saboda barin nasihata da na yi maku. All..ne mataimaki na a kanku’.

04-Imam Al-Hassan (a) a tafiyar da yayi zuwa Sham wata rana ya fita daga birnin Damashk sai ya dawo, sannan da ya dawo ya je ya shiga wajen Mu’awiya a fadarsa. Mu’awiya ya tashi ya gaida shi sai aka zauna, sai ya fadawa Imam kan cewa “ka gaji yakamata ka je ka huta” sai Imam (a) ya tashi ya sallameshi ya tafi.

Bayan fitarsa, sai Mu’awiya ya kira Abdullahi dan Zubair wanda yake cikin fadarsa a lokacinda Imam (a) ya shiga, sai yace masa. Me yasa ba zaka yi alfakhari a kan Al-Hassan ba? Kai dan makusancin Manzon All..(s) ne, ko hawarinsa, dan goggonsa. Kuma babanka yana da rabo babba a farkon musulunci.

Sai Abdullahi dan Zubair ya yaudaru da kha’incin Mu’awiya dan Abusuftan gareshi, sai ya bayyana masa kan cewa a shirye yake ya yi alfakhari kan Imam Al-Hassan (a).

Sai suka watse, sannan Abdullahi dan Zubair ya kwana a cikin dare yana tunanin abinda zai fadawa Imam Al-Hassan (a), idan sun hadu. Yana tunanin yanda zai sifantashi don ya rage matsayinsa, ya kuma daukaka kansa.

Sai ya shigo fadar Mu’awiya a goben, sannan suna zaune sai Imam Al-Hassan (a) ya shigo, sai Mu’awiya ya tashi ya tarbeshi ya kuma gaida shi. A lokacinda kowa ya zauna, sai Abdullahi dan Zubair ya tashi yana fara Magana, yana kuma aibata Imam Al-Hassan yana cewa:

“Idan ba  gazawa da kaskanci a yaki ba, ba jarumi ba, me ya kaika ga mika al-amuran shugabanci ga Mu,awiya dan Abusufyan? Da kuwa baka bukatar ka tasho daga wuri mai nisa, ka keta dazuzzuka ka zo kofar gidansa kana neman Al-Kairi a wajensa ba.

Ka dace da kada ka yi haka tunda kai dan Aliyu (a) ne, a jaruntansa a kuma kyautarsa, amma ban san abinda ya sa kayi haka ba. Raunine a tunaninka ? ko kum Rauni a halittar ka?. Bana tsammanin kana da mafita a wadannan halaye biyu ba.

Na Rantse da All..da na sami abinda ka samu, da ka san cewa ni dan Zibair, Lalle ba zan jada baya daga barin gwaraza ba, ta yaya ba zan kasance haka ba?, kakata it ace Safiyyatu dan Abdulmuttalib. Sannan babana Zubair dan Zababbun sahabban Manzon All..(s). Jarumi mafi tsanani a yaki, mafi kyawunsu a nasaba a Jahiliyya, mafi biyayyarsu ga Manzon All..(s). A lokacinda ya yi shiru, sai Imam Al-Hassan (a) ya tashi ya mayar masa da martani kan karyayyakinsa.

Yana cewa:

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted