Shugaban Iran Ya Ce Iran Tana Goyon Bayan Duk Abinda Falasdinawa Suka Zaba A Tattaunawa

Shugaban kasar iran Dr Masoud Pezeshkiyan yace yana goyon bayan Falasdinawa kan duk abinda suka zaba a tattaunawa zagaye na biyu tsakaninsu da HKI.

Shugaban kasar iran Dr Masoud Pezeshkiyan yace yana goyon bayan Falasdinawa kan duk abinda suka zaba a tattaunawa zagaye na biyu tsakaninsu da HKI.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a zantawarsa ta wayar tarho da shugaban bangaren siyasa na kungiyar Hamas Khalilul Hayyah a yau Laraba. Ya kuma kara da cewa, har yanzun a wajen Iran matsalar falasdinawa ita ce babbar matsala ga al-ummar musulmi.

Shugaban ya taya Khaliyul Hayyah jimamin shahadar Isma’il Haniyya da kuma shahadar Yahyah Sinwar a bayansa. Sannan ya taya shi murnin zabensa a matsayin sabon shugaban kungiyar. Ya kuma yi masa fatan al-khairi da gamu da katar na All..ta’ala a cikin ayyukansa.

Labarin ya kara da cewa, shugaban kungiyar ta Hamas ya yabawa JMI da ci gaba da goyon baya da kuma tallafawa kungiyar tun lokaci mai tsawo da kuma dorewa a kan hakan.

Ya kuma roki All..ta’ala ya bawa JMI nasara a kan makiyanta makiyan Falasdinawa a yakin da take fafatawa da Amurka da kuma HKI.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted