Fadar shugaban kasar Tunisia, ta sanar da korar firaministan kasar, Ahmed Hachami, ba tare da wani bayyani a hukumance ba.
A yammacin jiya Laraba ne aka kori firaministan, inda aka maye gurbinsa da ministan harkokin jin dadin jama’a Kamel Madouri da aka nada kwanan nan.
Ahmed Hachani, wanda aka kora, ya maye gurbin Najla Bouden a ranar 1 ga Agusta, 2023, wanda shi ma shugaban kasar Kaïs Saïed ya kore shi ba tare da wani bayyani ba.
Kafin nan dai Ahmed Hachani ya wallafa a ranar 7 ga watan Agustan nan wani bayyani kan taron da akayi na gwamnatin kasar, musamman kan mawuyacin halin da zirga-zirgar jama’a ke ciki a kasar.