Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ya soke hare haren da ya dauki aniyar kai wa a kasar iran, bayan da kasashen yankin suka bukaci yayi haka saboda yiyuwar cimma wata yarjejeniyar tsakani, da kuma barazanar da Tehran tayi na cewa idan aka kai mata hari to zata mayar martani mai tsakanin da ba’a taba ganin irinsa ba a baya.
A cikin bayanan da ya wallafa a shafinsa na truth social Trump yayi ikirarin cewa Amurka ta na cikin mawuyacin yanayi kuma tana shirin kai wa iran hari , kuma ya bayyana batun harin a matasyin wani abu da ya shafi karfin soja, wanda baa taba gani ba tun yakin duniya na biyu
Ana sa bangaren kakakin kwamitin tsaron kasa da tsare tsare na majalisar shawara ta kasar iran Ebrahim Reza’i yayi gargadin cewa tehran za ta mayar da martani kan duk wani hari da aka kawo mata kuma ba zai tsaya a yankin tekun fasha ba kawai zai kai inda baa yi tsammani na.
A lokacin guda masu shiga tsakanin na kasar Qatar sun yi tattaunawa ta daban da ministan harkokin wajen iran Abbas Araqci da wakilin Amurka Steve witkoff da jami’an kasar Oman a wani kokari da ake yi na cimma wata yarjejeniya game da batun bude mashigar Hurmuz