Shugaban Ghana John Dramani Mahama, ya kaddamar da sashen tace danyen mai da aka gyara a matatar mai ta Tema, matakin da ya kawo karshen tsaikon aiki da matatar ta fuskanta na tsawon lokaci saboda matsalolin kuɗi da na kayayyakin aiki.
A karon farko, matatar ta samu nasarar karɓa da kuma sarrafa gangar mai miliyan daya da aka haƙo daga filin mai na Jubilee na ƙasar Ghana.
Shugaba Mahama ya jaddada cewa wannan babban ci gaba ne da ke nuna cewa Ghana za ta iya tace nata man ba tare da dogaro da matatun ƙasashen waje ba.
yace wannan mataki zai rage matsin lamba akan kudin kasar Cedi, ta yadda zai daidaita farashin man fetur a kasuwa, sannan zai samar da guraben ayyukan yi da dama ga matasa.
Shugaba Mahama ya bayyana cewa burin gwamnatinsa shi ne ta fadada karfin matatar ta Tema don ta riƙa tace gangar mai 100,000 a kowace rana.
Shugaban ya bayyana cewa, gwamnati na shirin canza fasalin matatar baki ɗaya domin ta zama babbar cibiyar tace mai da za ta rika wadatar da yankin Afirka ta Yamma.