Rahotanni sun bayyana cewa muqaddashin ministan tsaro na kasar iran ya jaddada cewa kula da tsaron yankin ya kamata ya kasance a hannun kasashen yankin ne , don haka yana kira da a kafa rundunar tsaro ta hadin guiwa ta kasashen musulmi , kuma yayi wannan bayani ne a tattaunawa da suka yi ta wayar tarho da takwaransa na kasar Turkiya
Mukaddashin ministan tsaro na kasar Iran janar majid bin ridha ya fadi a yau litinin cewa kasancewar sojojin waje a yankin suna daga cikin abubuwan dake haifar da rashin tsaro da zaman lafiya, don haka akwai bukatar kafa rudunar tsaro tsakanin kasashen musulmi domin tabbar ta zaman lafiya ga yankin baki daya
Da yake magana game da batun dakatar da bude wuta kuma, ministan ya bayyana cewa jamhuriyar musulunci ta iran ta amince da rattaba hannu kan yarjejeniyar ne don ganin an samu daidaito a yankin, bisa bukatar da gwamnatocin dake makwabtaka da ita kuma a bokai suka gabatar, amma bisa la’akari da tarhin karya alkwari da kasar Amurka take da shi yasa ba zata amince da ita ba.
Yace dakarun sojin kasar Iran A shirye suke su mayar da martani mai tsananin kuma wanda ya dace kan duk wani mataki na keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma tsakanin, don kare tsaron kasarta