Falasdinawa 22 ne suka yi shahada yayin da wasu gwammai kuma suka jikkata a cikin saoi 24 da suka gabata sakamakon hare-haren da Isra’ila ta kaddama a yankin Gaza, a ci gaba da keta yarjejeniyr dkatar da bude wuta da take yi
majiyar Asbiti a yankin falasdinu ta sanar cewa wasu falasdinawa guda 2 sun yi shahada bayan da suka yi mafa da mummunan rauni da suka ji a harin da isra’ila ta kai ,su ne Ahmad muamin najjar wanda ya samu rauni kwanibiyu da suka wuce a jabaliya sai kuma said ahmad badash da ya samu rauni wata guda daya gabata
majiyar tace adadin wadanda suka yi shahada daga lokacin da aka sanya hannu kan yarjejeniyar dakatar da bude wuta zuwa yanzu ya kai falsdinawa 1230, yayin da 4076 kuma suka jikkata , yayin da adadin wadanda suka yi shahada daga lokacin kaddamar da yakin kare dangi kan alummar gaza daga watan oktoban shekara ta 2023 yakai shahidai 73356 tare da jikkatar 174185