Pezeshkiyan: Dole Ne Bangaren Amurka Ya Kiyaye Alkawali, Kafin Duk  Wata tattaunawa

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa takardan fahintar juna tsakanin Iran da Amurka, ita ce abin dogaro ga dukkan hulda da kasashen waje

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa takardan fahintar juna tsakanin Iran da Amurka, ita ce abin dogaro ga dukkan hulda da kasashen waje nan gaba, saboda majalisar koli ta tsaron kasar Iran ce ta amince da fahintar junan da ke cikin takardan.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a shafinsa na X a yau Litinin ya kuma kara da cewa, saboda fahintar junan sakamakon tunan manya manyan jami’an gwamnatin kasar Iran ne, zai zama nan gaba itace madogara wajen kulla dangantaka da kasashen waje.

Yace gwamnatin kasar Iran zata baje iya kokarinta don ganin makiya sun cika alkawulan da suka daukaa cikin wannan fahintar junan wacce suka rattabawa hannu.

 Yace aiwatar da abubuwan da suka zo cikin takardan fahintar Junan zai kai ga muradon kasar Iran da na kasashen yankin,har’ila yau shi zai tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a yankin yammacin Asiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted