Rundunar Sojin Najeriya ta tura sojoji 86 da za su yi aiki karkashin inuwar rundunar zaman Lafiya ta ECOWAS a Guinea-Bissau,wanda hakan ke kara karfafa hadakar Najeriya da sauren kasashen karkashin inuwar ECOWAS a batutuwan da suka jibanci zaman lafiya da tsaro a yankin.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafukanta na sada zumunta rundunar tsaron Najeriya ta ce sojojin sun tashi daga filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, da ke Abuja, a cikin jirgin saman Sojin na Najeriya C-130 Hercules inda aka bayyana cewa sun samu sauka a Guinea-Bissau,wanda za su soma aiki karkashin rundunar ta ECOWAS.
Wannan dai ba shine karo na farko da Najeriya ke taka rawa a abubuwan da suka shafi tabbatar da zaman lafiya da tsaro ba,ko a ƴan watanni da suka gabata ,sojojin Najeriya sun taimaka wajen dakile juyin mulki a Jamhuriyar Benin.
Daraktan Ayyukan Tallafawa zaman lafiya, Birgediya Janar MM Idris,ya umarci sojojin da su yi aiki a matsayin jakadun da suka cancanta na rundunar soji, rundunar sojojin Najeriya da kuma kasar ta hanyar aiwatar da ayyukansu da aminci, kiyaye dokoki da al’adun kasar Guinea Bissau, da kuma kiyaye rashin aikata laifukan da suka sabawa kasar.
Ta kara da cewa har yanzu tana daya daga cikin manyan masu bayar da gudummawa a Afirka ga ayyukan wanzar da zaman lafiya na yanki da na kasa da kasa, inda ta yi amfani da shekaru da dama tana aiki a karkashin ECOWAS, Tarayyar Afirka da Majalisar Dinkin Duniya.