Ma’aikatar sharia a nan kasar Iran ta tabbatar da cewa, ta zartar da hukuncin kisa kan mutane biyu wadanda suka yi aiki da HKI suka yi mata ayyukan leken asiri a lokacin yaki.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar kotun koli na kasar tana cewa, ta tabbatar da hukuncin da aka yankewa Omid Behzad da kuma Poria Safyat bayan ta tantance shaidun da aka gabatar a kansu.
Labarin ya kara da cewa Behzad ya yi amfani da woyarsa ta hannu inda ya aikawa HKI da kuma tashar talabijan ta ‘International’ hotuna da kuma inda jami’an tsaron JMI suke.
Hakama Safyad ya tabbatar da cewa ya yi amfani da Google Maps kan woyarsa inda ya turawa Jami’an MOSAD wurare jami’an tsaro a nan JMI tare da hotuna da kuma bidiyo na wuraren. Wadanda kuma daga baya Jiragen yakin HKI sun kai hare hare a kan wadan nan wurare.
Suka kai jami’an tsaro da dama ga shahada.
Masu gabatar da kara sun bayyana cewa mutanen biyu sun tabbatar da zargin da ake masu sun kuma sami shaidun da suke tabbatar da ikrarinsu da kansu a kan wayoyinsu da wasu wasu hanyoyi.