Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ci gaba da tattaunawa da tokwarorinsa a yankin yammacin Asiya dangane da matsalolin tsaro a yankin.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana cewa a cikin sa’o’i 24 da suka gabata ya tattauna ta wayar tarho da ministocin harkokin wajen na kasashen Saudiya, Pakistan da Iraki kan matsalolin tsaro na yankin.
Labarin ya kara da cewa Aragchi ya tattauna ta wayar tarko da ministan harkokin wajen kasar Saudia Faisal Bin Farhan, da kuma Janar Asim Munr babban hafsan sojojin kasar Pakistan har’ila yau da kuma Fu’ad Hussain ministan harkokin wajen kasar Iraki, a lokuta daban daban.
Jami’an gwamnatocin kasashen sun tattauna dangane da matsalolin tsaro a yankin da kuma inda aka kwana dangane da yakin da Amurka da kuma HKI suka fadawa Iran da shi a farkon wannan shekarar.
Labarin ya kammala da cewa ministan ya ci gaba da daukan matakan diblomasiyya a yankin ne don ganin an sake dawo da zaman lafiya a yankin tare da hadin kan dukkan kasashen yankin.