Iran Ta Musanta Tattaunawa Da Amurka, Ta Tabbatar Da Tattaunawa Da Omman Dangane Da Hurmuz

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa, babu wata tattaunawa da kasar Amurka kan yakin da ake fafatwa da ita, amma ta tabbatar da

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa, babu wata tattaunawa da kasar Amurka kan yakin da ake fafatwa da ita, amma ta tabbatar da cewa tana tattaunawa da kasar Omman amma shima dangane da mashigar ruwa ta Hurmuz ne kadai bai shafi yakin ba.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il bakaei yana fadar haka a yau Litinin ya kuma kara da cewa, babu tattaunawa da gwamnatin kasar Amurka kai tsaye ko tare masu shiga tsakani. Sannan tana tattaunawa da kasar Omman kan hanyoyin da jiragen ruwa zasu bi, na wucin gadi idan an sake bude mashigar nan gaba.

Ya kara jaddada cewa, tattaunawa da Omman dangane da zirga zirgan jiragen ruwa ne a mashigar ruwa ta hurmuz kuma bai da dangantaka da kasar Amurka ko kadan.

Baghaei ya ce, jita jita kan cewa, na rufe mashigar ruwa ta Hurmuz ne saboda sabani tsakaninta da Omman, ba gaskiya bane. Yace kafin yakin da Amurka da HKI suka dorawa Iran a ranar 28 gawatan Fabrayru babu wani sabani dangane da mashigar ruwa ta Hurmuz da kasar Omman. Kuma a halin yanzu kuma suna tattaunawa da ita ce saboda iran tana son tabbatar da ikonta a kan mashigar domin tsaron kasarta. Ya kuma musanta cewa wakilan kasashen Qatar da Pakistan suna halattan taron tattaunawa da kasar ta Omman.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted