Rahotanni sun bayyana cewa kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqai ya jaddada cewa tattaunawar da suke yi yanzu haka da kasar Oman ta mayar da hanakali ne kan abin da ya shafi tsaron mashigar Hurmuz , amma tahren bata wata tattaunawa da Amurka a halin yanzu.
Haka zalika kakakin ya jaddada cewa tattaunawa ta wayar tarho da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi yake yi a yankin, tana kokari ne wajen ganin an warware matsalar rashin tsaro ne dake addabar yankin, da kuma kare manufofin iran,
Isma’ila Baqa’I yace tattaunawar da aka yi jiya tsakanin iran da Oman wata tattaunawa ce da ta shafe su bata shafi wani daga waje ba, kuma ana tattaunawa ne domin lalubo mafita game da da batun tsaron mashigar Hurmuz da zaa cimma matsaya akai, yadda ba zai kasance makomar arewa ko kudu ba, zai kunshi abubuwan da zasu kare tsaron yankin da kuma masalahohin bangarorin guda biyu
Dagar karshe baqai yace game da batun tattaunawa da bangaren Amurka ,yace lallai iran bata wata tattaunawa da kasar Amurka a hanlin yanzu kuma dukkan mamabobin tawagar tattaunawar ma suna iran, kuma baa sanya cewa tawagar za su je wata kasa don tattaunawa ba.