Iran Ta Ce Makomar Hurmuz Na Tare Da Amincewa Da Ikon Kasar A Kanta Da Kuma Karshen Yaki

Gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa makomar mashigar ruwa ta Hurmuz bai takaita da tattaunawa da take yi da kasar Omman na samar da shirin

Jirgin ruwan Qatar Ya Wuce Ta Hurmuz

Gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa makomar mashigar ruwa ta Hurmuz bai takaita da tattaunawa da take yi da kasar Omman na samar da shirin wucin gadi na bude ta ba, sai dai dole ne ya hada da amincewa da cikekken ikon kasar Iran kan mashigar da kuma kawo karshen yakin da Amurka da HKI suka dorawa kasar.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baghaie yana fadar haka a yau Litinin. Ya kuma kara da cewa, tattaunawa da kasar Omman kadai bai wadatar wajen bude mashigar ba. Sai dai babban al-amarin shi ne yakin da Amurka da HKI suka dorawa kasar a farkon wannan shekarar.

Yace: Dole ne duniya ta amince da ikon kasar Iran a kan mashigar, sannan Amurka da HKI su kawo karshen yakin da suka dorawa kasar.

Baghaei ya kammala da cewa, dole ne sai an koma kan takardar fahintar juna da aka rattabawa hannu tsakanin Amurka da Iran a ranar 18 ga watan Yunin shekara ta 2026 tsakanin shuwagabannin Amurka da Iran, wanda ya bukaci kasar Iran ta shiryawa bude mashigar ruwa ta Hurmuz a cikin kwanaki 60. Sannan a kammala tattaunawa dangane da cikekken yarjeniyar zaman lafiya tsakanin kasashen biyu cikin watanni biyu.

Amma Amurka ta sabawa dukkan ci gaban da aka samu, inda ta sake farwa kasar da yaki, da killace harkokin kasuwanci na kasar Iran ta ruwa da kuma tada sabon yaki.

Yace matukar Amurka da HKI basu kawo karshen yaki kan kasar Iran ba, halin da ake ciki dangane da mashigar ruwan zai ci gaba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted