Shugaban kasar Amurka dan ta’adda ya fadawa tashar talabijan ta Foxnews kan cewa baya bukatar taimakon Beigin ko Mosco don kawo karshen yakin da yake fafatawa da Iran tun kimani mwatani 9 da suka gabata.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a hirarsa da Foxnews a jiya Laraba, kuma kafin taron shuwagabannin kasashen uku a cikin yan kwanakimasu zuwa.
Trump ya farwa kasar Iran da yaki a cikin watan Fabrayrun shekara ta 2026 da muke ciki, da nufin kifar da gwamnatin Jumhuriyar musulunci ta Iran (JMI), da kuma kawo karshen tsarin musuluncin da ke tafiyar da kasar, a cikin yan makonni amma a yau an kai kimani watani 9 babu alamun nasara, sai dai karaya da kuma rashin nasara sun bayyana a fili wajen cimma wannan manufofin.
Shugaban dan ta’adda ya fadawa Foxnew kan cewa a tsawon yakin da ya shiga da Iran kasashen Rasha da China basu yi wani abu na muzantawa Amurka ko taimakawa makiyinta a kasnta ba.
A wannan karon ma Trump ya sake nanata cewa, a halin yanzu mashigar ruwa ta Hurmuz na karkashin ikon Amurka, kuma suna jigilar danyen man fetur kamar yanda suka ga dama, al-hali labaran duniya a ko ina suna maganar konewar jiragen ruwa mashigar ruwa ta Hurmoz saboda sabawa umurnin Amurka a mashigar.