Kasashen Iran Rasha da kuma China sun bada sanarwan hadin giwa wanda yak e nuna cewa jami’an hukumar makamashin Nukliya ta duniya wato IAEA ba zasu koma aikin bincike a kasar Iran ba sai an kawo karshen yakin da Amurka da HKI suka dorawa kasar, a kuma samar da lamunin cewa ba za’a sake fada mata da yaki ba.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kasashen uku na fadar haka a jiya Laraba a wani bayanin da suka gabatarwa gwamnonin hukumar IAEA a Vienna. Bayanin ya kara da cewa, hare haren da Amurka da HKI suka kai kan cibiyoyin makamashin Nukliya na kasar Iran a yakin kwanaki 12 wato a cikin watan Yunin shekara ta 2025 da kuma na watan Fabrayrun shekara ta 2026
Sun sabawa dukkan dokokin kasa da kasa musamman na hukumar ta IAEA. Don haka da farko dole a kawo karshen yaki a kan kasar Iran sannan a samar da yanayin babu wata barazana a kan cibiyoyin makamashin nukliya na kasar Iran , tare da lamunan ba za’a sake kai mata wasu karin hare hare ba kafin a yi maganar dawowan ma’aikatar hukumar IAEA zuwa Iran don ci gaba da bincike.
Daga karshe sun bayyana cewa, kamalan shugaban hukumar ta IAEA sun taimaka wajen ruruta yaki a kan kasar ta Iran a yake yaken da suka dorawa a kasar na watan Yuni da kuma Fabrayru na wannan shekara.