A dai dai lokacinda aka tambayi manya manyan jami’an tsaro a nan Jumhuriyar Musulunci ta Iran (JMI) dangane da halin da ake ciki a kasar da kuma yankin dangane da yakin da ake fafatwa da Amurka, sun bayyana cewa a abinda yake bayyane a fili shi ne Amurka ta kasa cimma mummunan manufofinta kan JMI, sannan bayyana wasu al-amura masu muhimmanci da ke faruwa.
Ka,fanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya kara da cewa, masana harkokin yaki na kasashen yamma sun tabbatar da cewa, lallai akwai sauyi a cikin yanda al-amura suke tafiya a duniya, bayan fara yaki da Iran , kuma ya tabbata a fili Amurka ta kasa cimma manufarta na mamayar kasar Iran bayan ta sauya gwamnatin kasar, sannan sun tabbatar da cewa JMI ta dogara da karfin soja da kuma makamanta na cikin gida ne a yakin da take fafatwa da Amurka na tsawon wattani kimani 9da suka gabata.
Labarin ya nakalto masu sharhi kuma masana abinda ke kaiwa ya komo dangane da yakin sun tabbatar da cewa shugaba Trump yayi fushi kan rashin samun nasar a wannan yakin musamman bayan da yakin ya janyo faduwar Jam’iyyarsa ta republican a zaben tsakiyar wa’di da aka gudanar a farkin wannan watan.
Sannan sun tabbatar da cewa Trump ta fada cikin Tarkon Natanyahu Firay ministan HKI, a lokacinda ya amince ya shiga yaki da kasar Iran. Ya kuma yi nadamar hakan, ya kuma yi fatan, ina ma bai shiga wannan yakin tun farko ba. Sannan a halin yanzu bai da wata mafita wacce zata bashi nasar a wannan yakin. Ya zama masa dole ya amince da wasu ko dukkan sharuddan Iran na kawo karshen yakin, wanda kasksanci ne wanda bai taba tsammanin zai taba faruwa da shi ba.