Kungiyar kula da ma’aikatan janya da unguwar zoma ta yankin falasdinu ta bayyana cewa kimanin ma’aikatan jinya da uguwar zoma kwararru guda 1700 ne isra’ila ta kashe a hare haren da take kai wa a yakin kare dangi da ta shelanta a yankin gaza
Kungiyar ta fitar da wannan bayanin ne a jiya laraba inda ta yi kira ga majalisar dinkin duniya da ta dauki mataken da suka dace wajen kare ma’aikatan lafiya da kuma tantance makomar wadanda suka rage a yankin Gaza
Haka zalika kungiyar ta kara da cewa likitoci da ma’aikatan jinya har yanzu suna kulawa da marasa lafiya, duk da irin mataken da isra’ila ke dauka na kashe su da kuma matsalar karanci kayayyakin aiki da ake fama da shi
Tun a watan oktoban shekara ta 2023 da isra’ila ta kaddamar da yakin kare danga a yankin gaza, sama da falasdinawa 74000 ne suka mutu yayin da suka jikkata 175000 kuma mafi yawancinsu mata ne da yara kanana kamar yadda ma’aikatar lafiya ta yankin gaza ta sanar