Iran A Athen Ta Musanta Zargin Ayyukan Ta’addanci

Ofishin jakadancin jumhuriyar Musulunci ta Iran a birnin Athen na kasar Girka ya bada sanarwan cewa zargin cewa Iran tana ayyukan ta’adanci a kasar ba

Ofishin jakadancin jumhuriyar Musulunci ta Iran a birnin Athen na kasar Girka ya bada sanarwan cewa zargin cewa Iran tana ayyukan ta’adanci a kasar ba gaskiya bane.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto majiyar Ofishin jakadancin na cewa, wannan zargin yakin farfaganta ne wanda haramtacciyar kasar Isra’ila take ci gaba da kan kasar, kuma ba saboda bane. Amma gaskiyar al-amarin shi ne Tehran bata shirin aiwatar da wani aikin taaddanci a kasar kuma karya ce a cikin tsarin yaki da Iran wadanda makiyanta musamman Isra’ila suke shiryawa .

Kafin haka dai wasu kafafen yada labarai na kasar Girka, da na arewacin Macedonia da kuma wasu kasashen yamma sun yada labaran karya na cewa wata jama’a wacce take samun goyon bayan Iran sun shirya aikin ta’addanci na kashe wani dan kasuwa bayuhuden Isra’ala a cikin kasar.

Kuma wannan farfagandar yasa aka kama wasu mutane a matsayin wadanda ake tuhuma kan shirin, da kuma korar wasu daga arewacin Macedonia, wanda dama karya ce aka shirya.

 Don haka Iran tana kira ga kasashen duniya wadanda suka damu da abinda yake faruwa su dauki cewa wannan ma wani nau’ii ne nay akin da ke tsakanin jumhuriyar Musulunci ta kasar da kasashen yamma.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted