Nahiyar Afrika Na Asarar Biliyoyin Daloli Duk Shekara

nahiyar afrika na fuskantar asarar biliyoyin daloli a duka shekara saboda harkokin da suka kauce hanya

Hukumar  yaki da rashawa ta Afrika, ta ce kasashen nahiyar na tafka hasarar kimanin Dala biliyan 125, sakamakon hada-hadar kudade ta haramtattun hanyoyi, yayin da kuma wasu biliyoyin Dalar ke zurarewa a dalilin cin hanci da rashawa.

Baya ga hasarar Dala biliyan 125, kwatankwancin Naira Tiriliyan 169 a dalilin haramtattun hanyoyin da ake bi wajen hada-hadar kudaden, kasashen na Afrika na tafka ƙarin hasarar karin Dala biliyan 80 sakamakon matsalar cin hanci da rashawa, lamarin da ke nuna cewar aƙalla kaso 50 cikin 100 kenan na jimillar kudaden shiga nahiyar ta Afrika ke rasawa a duk shekara.

Yayin gabatar da wadannan alkaluma a Abuja babban birnin Najeriya, shugaban hukumar yaki da rashawar ta Afrika Honorable Kwami Senanu, ya bukaci daukar matakan gaggawa domin kwato dimbin kadarori da kudaden da aka karkatar domin amfani da su ta hanyoyin da suka dace. Dan haka kamata ya yi kasashen Afrika su fara aiwatar da alƙawuran da suke dauka a aikace, sabanin nanata alwashin da ke tsayawa a furucin baka kadai.

Gagarumar hasarar da kasashen na Afrika ke tafkawa dai na fayyace yadda hada-hadar kudade ta hanyoyin da basu dace ba, ke dakile muradun cigaba da ya kamata a ce an dade da cimmusu, gami da kyautata rayuwar miliyoyin ƴan nahiyar ta Afrika.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted