Shugabannin kasashen China da Rasha da kuma Amurka sun yi wata kebantacciyar ganawa a yau Alhamis a gefen taron tattalin arziki da hadin kan kasashen Asia da Pacific wanda ke gudana a birnin Shenzhen na China,
A wani yanayi da Turai ke fargabar abin da shugabannin 3 ka iya cimmawa a wannan ganawa, an jiyo shugaba Donald Trump a ganawarsa da shugaba Xi na cewa China na da rawar da zata iya takawa don dakatar da yakin Ukraine, yayinda a nata bangaren Beijing ke neman kawar da hankalin Washington daga lamurran da suka shafi Taiwan da ta ce shi kadai ka iya kawo tarnaki ga kawancen kasashen biyu.
A gefe guda kuma sanarwar da Kremlin ta fitar ta ce ganawar Trump da Putin ta tsawon minuna 40 a safiyar yau ta mayar da hankali kan yakin na Ukraine sai dai babu bayanai kan yiwuwar sararawar Moscow don dakatar da yakin.
Babu dai tabbacin shugabannin 3 su amince da dukkanin tayin da zasu yiwa junansu, la’akari da sabanin da ke tsakaninsu a batutuwa da dama, musamman daga bangaren Xi da ke fatan Rasha da Amurka su dakatar da kera manyan makamai masu hadari, sai dai babu tabbacin kasar ta amince da tayin Amurka na shiga yarjejeniyar nukiliya a tsakaninsu su 3.