Babban kwamandan rudunar sojin kasar iran Major Ganaral Amir Hatami yayi gargadin cewa duk wani kuskuren lissafi da makiya za su yi kan kasar iran to zai hadu da mummunan mayar da martani mai tsanani , yace iran zata mayar da martani da dukkan karfinta kan duk wani hari da makiya zasu kawo mata
Janar Hatami yayi wannan gargadin ne a daidai lokacin da hankula ke kara tashi a yankin da kuma isar wani sabon jirgin yakin amurka a yankin yammacin asiya , yayi gargadin cewa Tehran tana ci gaba da bibiyar ci gaban da ake samu, kuma ba za ta yi kasa a guiwa ba game da kasancewar sojojinta cikin shirin ko ta kwana ba
Hakazali yace kowanne bangare na rundunar sojin iran da suka hada da sojojin sama da na ruwa dana kasa suna kara sa ido sosai game da take- taken makiya kuma kowane lokaci sun kara zama cikin shirin ko ta kwana ne
Daga karshe babban kwamandan yace muna fatan makiya ba za su yi irin wannan kuskuren lissafin ba, amma idan suka yi to za su dauki darasi da zai zama babban gargadi ne ga kowa.