Shugaban tarayyar Najeriya, Bola Tinubu ya bada sanarwan kara fadada wuraren da zai je don yakin neman zabe a kasar, ya kuma fidda jihar Bauchi daga cikin jihohin da zai ziyarta don haka.
Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta nakalto majiyar kwamitin yakin neman zaben shugaban yana cewa a halin yanzu abinda yake gabansu shi ne, yawan jihohin da zasu je yakin neman zabe ya karu daga 12 zuwa 19 bayan babban birnin tarayyar kasar Abuja.
Kwamin yay akin eman zaben shugaba na jam’iyyar APC ya kara da cewa shugaba Tinubu zai halarci wuraren yakin neman zaben a wa’adi na biyu a wurare 20 aduk fadin kasar.
Kuma a halin yanzu zasu aiwatar da wannan shirin ne daga ranar 24ga watan Octoba zuwa 13 ga watan Jeneru na shekara ta 2027.
Sannan an kara yawan jihohin da shughaban zai ziyarta don yakin neman zaben wadanda suka hada da Katsina, Taraba, Zamfara, Imo da Kwara, har ila yau an hada da Akwa Ibom da Jigawa da kuma Kebbi a cikin karin.
Sannan a cikin sabon tsarin wasu manya manyan yan siyasa ne zasu wakilci shugaban a wasu jihohi.
Kafin wannan sabon shirin dai shugaba Tinubu ya bayyana a yakin neman zabensa a wa’dina biyu a Uyo a ranar 6 ga watan Nuwamban da muke ciki, a jihar Akwa Ibon, inda ya gabatar da