Iran Ta Soki Kasashen Yankin Da Amurka Ke Amfani Wajen Kai Mata Hari

kasar iran ta soki kasashen yankin da amurka ta mayar karamar katanga wani kai mata hare hare

Rahotani sun bayyana cewa Tehran ta yi kira ga kasashen yanki da su hana Amurka yin amfani da kasashensu a matsayin tsani na kai mata hari ne, mai makon su koma suna sukar iran a matakin da take dauka na kare kanta da dokoki suka bata

Maikatar harkokin wajen kasar iran ta fitar da wannan bayani ne a yau Alhamis adaidai lokacin da ake ci gaba da musayar bude wuta tsakanin iran da amurka, bayan da yarjejeniyar da aka cimma ta kawo karshen yaki take karewa ta shiga wata na 9

Ma’aikatar ta yi tir da mataken da kasashen yanki suka dauka na sukar iran game da hakkinta na kare kanta adaidai lokacin da suka rufe idonsu game da gaskiyar abin dake faruwa na hare-haren wuce gona da iri da kasar Amurka take kai mata

Daga karshe ministan harkokin wajen kasar iran ya jaddada matsayin iran na girmama hakki da iyakokin kasashen yankin dake yammacin asiya, kuma yayi tir da hare- haren soji da kasar amurka ta kai a wasu wurare dake kudancin iran a baya bayan nan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted