Tafiyar Dr. Araqchi zuwa kasar Sin

Ministan harkokin wajen Iran, Seyyed Abbas Araqchi, zai kai ziyara birnin Beijing a yau Talata, ranar 6 ga watan Mayu, 2026, a daidai lokacin da

Ministan harkokin wajen Iran, Seyyed Abbas Araqchi, zai kai ziyara birnin Beijing a yau Talata, ranar 6 ga watan Mayu, 2026, a daidai lokacin da ake ci gaba da takun saka tsakanin Amurka da Iran game da yakin da Isra’ila da Amurka suka kaddamar a ranar 28 ga watan Fabrairu.

A wannan ziyara da aka gayyace shi, Dr. Araqchi zai gana da babban jami’in diflomasiyyar Sin, Wang Yi, domin tattauna hanyoyin karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma halin da ake ciki a yankin da ma duniya baki daya.

Wannan tafiya tana zuwa ne a daidai lokacin da Sin ke kara fito fili wajen nuna goyon bayanta ga Iran. A karshen mako, ma’aikatar kasuwanci ta Sin ta umurci kamfanonin kasar da su bijirewa takunkumin da Amurka ta kakaba wa masu tace mai na Iran, inda ta yi amfani da wata sabuwar doka da ke ba ta ikon ramuwa kan duk wata hukuma da ta aiwatar da takunkumin da Sin ta dauka a matsayin sabawa doka.

Wani bangare na wannan yunkuri na diflomasiyya, Shi ne yunkurin da Sin take yi na mayar da kanta a matsayin mai sasantawa a rikicin. Sai dai a daya bangaren, wasu jami’an gwamnatin Trump kamar Sakataren Baitulmalin Amurka, Scott Bessent, sun bukaci Sin da ta kara kaimi wajen matsawa Iran lamba domin bude mashigar Hormuz, wadda take da matukar muhimmanci ga jigilar mai a duniya.

Hasali ma, wannan ziyara wani bangare ne na rangadin da Dr. Araqchi ya fara a yankin, inda ya riga ya kai ziyara Moscow, Islamabad, da Muscat, domin samun goyon baya da kuma hada kai da manyan kasashen da ake kallon su a matsayin masu adawa da Amurka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted