Sudan Ta Zargi Daular Larabawa Da Alhakin Baiwa RSF Horo

kasar Sudan ta zargi hadaddiyar daular larabawa da daukar nauyin bawa kungiyar RSF horo a habasha

Kasar Sudan ta sabunta zargin da take yi kan mahukuntan Habasha game da taimako ko kuma daukar nauyin mayakan RSF bayan da gwamnatin yankin Kurmuk ta bayyana cewa dandazon mayakan na RSF sun isa wani sansani na musamman a gab da iyakar kasar da Addis Ababa don samun horo.

Abdelati Mohamed El Faki, kwamishinan yankin Kurmuk na kudu maso gabashin yankin Nilu, ya yi zargin cewa dandazon mayakan ya isa sansanin Fana da ke Beninshangul-Gumuz a Lahadin da ta gabata, bayan sauka a filin jirgin saman Assosa na makwabciyar tasu.

El Faki ya yi zargin cewa, Hadaddiyar Daular Larabawa ce ta jagoranci aikin jigilar mayakan zuwa Habasha don samun horon.

Baya ga mayakan na RSF da kasashen na Daular Larabawa da kuma Habasha ke baiwa horo, Sudan ta kuma yi zargin cewa akwai sojojin haya na musamman da aka dauko wadanda suma aka horar da su don shiga yakin na kusan shekaru 4.

Duk da cewa babu cikakken hujjoji kan zargin na Sudan kan Habasha da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Laraba, amma wannan ba shi ne karon farko da Khartoum ke zargin Abu Dhabi da daukar nauyin yakin ba wajen baiwa RSF makamai da kudaden, kodayake kasar ta yankin Gabas Ta Tsakiya tana ci gaba da musantawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted