Araqchi: Komawar Amurka Kan MOU Ta Islamabad Da Farko…

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa komarwa Amurka kan takardan fahintar juna ta Islamabad shi ne matakin farko na sake dawo

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa komarwa Amurka kan takardan fahintar juna ta Islamabad shi ne matakin farko na sake dawo da zaman lafiya a yankin yammacin Asia.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na JMI ya nakalto Aragchi yana fadar haka, a lokacinda yake zantawa ta wayar tarho da tokwaransa ta kasar Japan Toshimitsu Motegi a yau talata.  

Labarin ya kara da cewa ministocin biyu sun tattauna al-amura da suka shafi kasashen biyu da kuma na yankin da kuma na kasa da kasa. Aragchi ya danganta halin da ake ciki a yankin yammacin Asia da abinda Amurka tayi na ficewa daga yarjeniyar fahintar juna ta Islamabad bayan yakin kwanaki 40 ko yakin Ramadan.

Ministan ta kammala da cewa, idan ana son kawo karshen halin da ake ciki a yankin, to kuwa dole ne Amurka ta koma kan MOU na Islamabat, kuma shi ne matakin na farko na rage tashe tashen hankula da suke faruwa a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted