Babban kwamandan sojojin kasa na JMI ya bayyana cewa sojojinsa suna sanya ido a kan iyakokin kasar dare da rana, kuma ba zasu bar wani motsi ko menene karancinsa daga wajen matsakiya su karato kan iyakokin kasar ba.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Ali Jahanshahi yana fadar haka a garin Zanjan.
Labarin ya kara da cewa Janar Jahanshahi ya bayyana haka ne a lokacinda yake ganawa da gwamnan lardin Zanjan, ya kuma kara da cewa, shojojinsa a shirye suke su tabbatar tsaron kan iyakokin na kasar Iran dare da rana ba tare da ghafala ko kadan ba.
Janar Jahanshahi ya kara da cewa aikin sojojin kasa a wannan lokacin mai hatsari wanda JMI ta shiga yana da muhimmanci. Don haka babu sako sako da aikin sojojin kasa na tabbatar da tsaro a ciki da kan iyakoki JMI.
A cikin ziyarar da babban kwamandan jojin kasan ya kai Zanjan ya ziyarci runduna ta 216 na shahid Gholamreza Mukhbiri Zanjan don ganewa idanunsa yanda suke tafiyar da aikinsu.