Dakarun kare juyin musulunci na iran sun sanar cewa sun kai mummunan hari a sansanin sojin Amurka dake Al-azraq a kasar Jodan da makamai masu linzami, da kuma kan jirgin ruwan na yaki na Amurka ,kuma ta bayyana harin a matsayin mayar da martani kan harin da sojojin Amurka suka kai kan tankokin mai na kasar iran
A cikin wani bayanin da bangaren hulda da jamaa na dakarun na IRGC suka fitar sun bayyana cewa a harin sun yi ruwan bama bamai a kan sansanin, kuma ya kunshi makami mai linzami mai karfi da aka harbasu a wuraren da sojojin Amurka ke gudanar da gyara gayrensu da wajen adana jiragen sama na yaki kirar F-35 da kuma F-15 da kuma F-16
Dakarun kare juyin sun danganta halin da ake ciki da yanayin mashigar Hurmuz, suka ce ci gaba da jajircewa da dakarun ke yi a cikin tekun ya jefa Amurka cikin matsatsi, domin Washington ba ta yi tsammanin za ta fuskanci muggan hare hare da aka kai mata ba.
Daga karshe dakarun sun ce za su ci gaba da kaddamar da hare-hare har sai sun kawo karshen hare haren da Amurka take kai musu, don haka wannan yakin zai ci gaba gudana har cin nasara