Kakakin sojojin kasar Yemen ya bada sanarwan kakkabo jirgin Drone na kasar Saudia karo na 3 a cikin sa’ai 24 da suka gabata.
Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya nakalto burgedia Yahyah Saree yana fadar haka a jiya litinin kan cewa sojojin kasar sun kakkabo makamin Drone samfurin Wing Loong II a dai dai lokacinda yake kai hare hare a lardin Al-Baida.
Saree ya kara da cewa wannan shi ne makamin Drone na kasar Saudia da muka kakkabo a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata.
Gwamnatin kasar Yemen ta San’a ta bada sanarwan killace jiragen ruwan dakon main a kasar Saudia a watan Yulin da ya gabata, har zuwa lokacinda zata dauke mata takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata na tsawon shekaru 12 da suka gabata.
Kafin haka a shekara ta 2015 kasar Saudia da kawayenta suka farwa kasar Yemen da yaki da sunan maida Abdurabbu Mansur hadi kan kujerar shugabancin kasar, amma bayan fafatawan da babu nasara na shekaru 8 an tsagaita wuta, ammam kuma ta ci gaba da dorawa kasar takunkuman tattalin arziki ta sama da kasa da ruwa.