Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a tattaunawarsa ta farko da sabon babban sakataren kungiyar kasashen musulmi ta OIC, ya taya shi murnar zabensa a matsayin babban sakataren kungiyar ya kuma yi masa fatan alkhairi a ayyukansa.
Kamfanin dillancin labaran (Tasnim) na kasar Iran, ya nakalto Aragchi yana cewa akwai bukatar sabon babban sakataren yayi amfani da matsayin da All..ya bashi ya hada kan kasashen musulmu don aikata abinda ya dace na kawo ci gaban kasashen musulmi da kuma warware matsalolin da suke fuskanta.
Ministan ya ce a halin yanzu matsalar al-ummar falasdinu ce ta fi damun kasashen duniya daga ciki har da kasashen musulmi da farko. Ya kuma yi fatan ganinsa a nan Tehran nan ba da dadewa ba.
Isma’il Ould Sheikh Ahmed dai tsohin ministan harkokin wajen kasar Mauritania ne, kuma jami’ann diblomasia wanda ya taba rike matsayin jakadan MDD na musamman kan al-amuran kasar Yemen.