Rahotanni sun nuna cewa kasashen masar da Jodan sun yi lale marhabin da matakin da kasar birtaniya ta dauka na hana yin harkokin kasuwanci da sauran hidimomi da sabbin garuruwan yahudawa yan share wuri zauna da isra’ila ta gina ba bisa kaida ba a yankunan falasdinawa da ta mamaye.
Haka zalika kasashen biyu sun bayyana wannan mataki da gwamnatin birtaniya ta dauka a matsayin muhimmi matuka, wanda yayi daidai da dokokin kasa da kasa da kuma kudurorin da majalisar dinkin duniya ta fitar na kalubalantar ci gaba da fadada gine gine isra’ila da kuma nisantar abin da zai raunata hanyoyin da kasashen biyu ke amfani da shi
shuwagabannin kasashen birtaniya ,faransa da kanada a cikin wani bayanin hadin guiwa da suka fitar ya nuna cewa fadada matsugunnan yahudawa yan share wuri zauna barazana ce kai tsaye ga zaman lafiya a yankin, kuma sun jaddada game da muhimmanci haramta shigar da kaya cikin garuruwan da aka yi ba bisa ka’ida ba da kuma sanya musu iyaka ga masu amfani da damar,
Yazo a cikin bayani da suka fitar cewa shekara guda da ta wuce mun amince da falasdinu a matsayin kasa mai cin gashin kai, yanzu lokaci yayi tun kafin ya kure a fara aiki da nauyin da ya taraya wajen kafa kasashen biyu masu cin gashin kai, kuma akwai bukatar daukar karin matakai don kare muradu da kuma dabiu a yankin.