Majalisar ministocin kasar sudiya da take mayar da martani kan hari da dakarun sojin kasar yamen suka kai musu a jiya, sun yi ikirarin cewa kasar saudiya za ta ci gaba da kare gwamnatin kasar da kuma zaman lafiyar alumma da mazauna kasar ta saudiya
haka zalika majalisar ta yi ikirarin cewa dakarun sojin kungiyar huthi sun kaddamar da hare haren a cibiyoyin da ban a soji ba da kuma bangaren tattalin arziki na kasar Saudiya.
Sai dai wannan ikirarin yana zuwa ne adaidai lokacin mohammad farah mamba a ofishin siyasa na kungiyar Ansarullah na kasar Yamen ya kore duk wani zargin kai hari kan wuraren da ban a soji ba, a kasar saudiya, yace hare harenmu yana daga cikin hakkokinmu na mayar da martani kan hare haren da Saudiya ta kawo ma kasar Yamen
Haka zalika ya kara cewa babu gaskiya kan batun kai harin kan wuraren da bana soji ba acikin kasar saudiya kuma babu wani abu mai suna gamayyar larabawa ko kuma dakarun sama na kasar yamen dukkan wadanan ikirari karya ce kawai suke yi da kuma kokarin boyewa a bayan labaran karya.