Gwamnatin kasar Burtania ta kara fadada takunkuman tattalin arziki na bangare guda wanda dama ta dade da dorawa JMI.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya ce, kamar yanda aka santa da nuna tsananin adawa da JMI gwamnatin kasar Burtania a wannan karon ma ta fadada takunkuman da ta dorawa kasar wadanda suka hada da kudade, harkokin kasuwanci da kuma zirga zirgan jiragen sama.
Labarin ya kara da cewa, a wannan karon Burtania ta fadada takunkuman tattalin arziki wanda ya hada da jiragen ruwan, sannan ta kara tsuke hanyar mu’amala ta kudade da tsarin kudade na kasar Burtania, a bangaren kasuwanci kuma ta kara rege yawan kayakin kasuwanci tsakanin kasashen biyu, kuma a halin yanzu sun hada har da ilmin kimiya lissafi na kayakin lantarki, da kuma dukkan ayyukan gyaran jiragen sama da sauran injuna.
A bangaren zirga zirgan Jiragen sama kuma Burtania ta haramtawa jiragen saman Iran sauka a kasar Burtania sai tare da izini na musamman.
A lokacinda yake kokarin dalilin daukar wannan matakan na nuna adawa da JMI sakataren ma’aikatan harkokin wajen kasar burtania Stephen Doughty ya ce sun yi haka ne don hana Iran mallakar makaman Nukliya.