Iran: Harin Amurka Da Isra’ila Ba Zai Lallata Shirin Nukiliyarta Ba

iran take hare haren da amuraka da israla ke kai mata ba zau iya yin wani tasirin kan shirinta na nakiliya ba

Rahotanni sun bayyana cewa kai hari kan cibiyoyin nukiliyar iran da kuma kashe masana  ilimin nukiliyar kasar, bai iya rusa shirin nukiliyar iran ba, ya jaddada cewa kwarewar ta ta nukiliya ta samu Asali ne bisa dogaro da Ilimi, kudiri da kuma albarkacin yawan alumma da take da shi

Wakilan iran sun halarci taron manya jami’in hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ne da aka yi a birnin Viyanna kuma sun yi wannan bayani ne a cikin jawaban da suka yi da aka fitar a jiya talata inda suka ce shirin nukiliyar Iran ba gini ko naurori ba ne kawai.

Haka zalika yazo a cikin jawabin cewa hare-haren Amurka da isra’ila kan kasar iran a shekarata 2025 da 2026 zai iya lalata cibiyoyin nukiliyarmu na zaman lafiya, kuma ya shafi damar da ake da ita ta amfani da fasahar nukiliya da wasu muhimman bangarori, sai dai karfin nukiliyar iran ya samo asali ne daga ilimi da kuduri da kuma albarkacin jama’a da kasar ke alfahari da su.

Bayani yayi ishara da wasu muhimman ayyuka da iran ke yi da shirinta na nukiliya da suka hada da bangaren Noma  kula da mahalli,inganta amfanin gona , magance kwari da cututtuka, kiyaye abinci da kuma amfani da ruwa da takin zamani yadda ya kamata

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted