CNN:Amurka Ta Fara Tunanin Rage Yawan Sansanoninta Na Soja Daga Gabas Ta Tsakiya Bayan Hare-haren Iran

Tashar talabijin din CNN ta Amurka ta yi rahoto wanda yake cewa; Gwamnatin kasar ta fara nazarin rage yawan sansanoninta na soja a cikin yankin

Tashar talabijin din CNN ta Amurka ta yi rahoto wanda yake cewa; Gwamnatin kasar ta fara nazarin rage yawan sansanoninta na soja a cikin yankin gabas ta tsakiya bayan da Iran ta yi ma ta barna mai yawan gaske.

Rahoton na CNN ya kuma bayyana cewa; sojojin Amurka da kuma jami’an harkokin tsaro, suna tattauna hanyoyin rage sojojin Amurka a cikin gabas ta tsakiya.

Har ila yau rahoton ya bayyana cewa; yaki da Iran ya bayyanar da raunin sansanonin Amurka a cikin wannan yankin bayan hare-haren da aka kai musu da makamai masu linzami da kuma jiragen sama marasa matuki.

 A gefe daya jami’an Amurka sun yi furuci da cewa hare-haren na Iran sun rushe Babbar cibiyar kungiyar leken asiri ta Amurka “CIA” dake birnin Riyadh a kasar Saudiyya.

Haka nan kuma  Iran din ta tarwatsa da lalata sansanonin sojan Amurka a kasashen Bahrain, Qatar, Saudiyya da Kuwaiti.

Kwamandan rundunar sojan Ruwan Amurka Admiral Daryl Caudle ya ce; sojojin na Amurka ba za su koma matsuguninsu dake kasar Bahrain cikin lokaci kankane ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted