Sudan ta nemi duka ‘yan kasar waje su fice daga birnin Khartoum cikin kwana 10.
Kamfanin dillancin labarai na Sudan (Suna) ya ruwaito “Shugaban sashen ‘yan kasar waje da kuma shige da fice a Khartoum, Kanar Nizar Khalil, ya bai wa ‘yan kasar wajen umarnin fita daga Khartoum cikin kwana 10 domin kare tsira da rayukansu daga yaki.
Akasarin birnin na Khartoum – da ya hada da tsakiya da kuma biranen unguwannin Bahri da Omdurman – na karkashin ikon RSF, kungiyar da take ta yaki da dakarun gwamnatin kasar tun Afrilun 2023.
Gwamnatin kasar dai jima tana mai zargin ‘yan kasar waje da taimaka wa kungiyar ta RSF.
A ranar 8 ga watan Yuli hukumomi sun tsare ‘yan kasar waje 154 da ake zargi sun shiga ta barauniyar hanya, Sai dai RSF ta musanta zargin.
A wani labarin kuma bangarorin da ke rikici da juna a Sudan din sun isa birnin Geneva na kasar Switzerland domin tattaunawa kan ”yiwuwar tsagaita wuta a kasar” wanda MDD ta shirya da nufin saukaka ayyukan jin kai da kare fararen hula, in ji mai magana da yawun MDD.
Yakin Sudan, wanda ya barke a watan Afrilun 2023 ya tilasta wa mutane kusan miliyan 10 barin matsugunansu, lamarin da ya haddasa barazanar yunwa da rikice-rikice na kabilanci wadanda aka dora alhakinsa kan kungiyar (RSF).