Shugaban mayakan RSF a Sudan Mohammed Hamdan Dagalo ya yi rantsuwar shugabatar gwamnati mai kishintar gwamnatin kasar.
Sanarwar ta ce Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti, wanda kuma ba kasafai ake ganinsa a kasar Sudan ba tun bayan barkewar rikici na tsawon watanni 28 tsakaninsa da sojojin kasar, an rantsar da shi ne a yayin wani biki a birnin Nyala na kasar Sudan, ko da yake kamfanin dillancin labaran Reuters ya kasa tabbatar da inda yake.
Nyala, daya daga cikin manyan biranen kasar Sudan dake yankin Darfur, wanda kuma shi ne babbar tungar mayakan kungiyar RSF, kungiyar da ta nada nata firaminista da majalisar shugabancin karkashin jagorancin Dagalo.
A ranar 16 ga watan Afrilu, Dagalo, kwamandan rundunar RSF ya shelanta kafa abin da ya kira gwamnatin zaman lafiya da hadin kai, wadda ya kira gwamnatin Sudan ta gaskiya.
A ranar 26 ga watan Maris, kungiyar ‘yan tawayen Sudan ta Rapid Support Forces (RSF) da kungiyoyin da ke kawance da ita, suka rattaba hannu kan kundin tsarin mulkin rikon kwarya da ke share fagen kafa gwamnati mai kiyantar juna da gwamnatin kasar.