Majalisar Gudanar da mulkin Sudan ta zargi dakarun kai dauki gaggawa da aikata kisan kiyashi a kauyen Wad Al-Nura
Majalisar Gudanar da mulkin Sudan ta zargi dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces da aikata kisan kiyashi kan fararen hula da dama a kauyen Wad Al-Noura da ke jihar Aljazeera a tsakiyar kasar.
Kwamitocin ‘yan gwagwarmaya da sukegoyon bayan sojojin kasar ta Sudan sun ce adadin wadanda suka mutu a hare-haren da Dakarun kai daukin gaggawa suka kai kan kauyen zasu iya kaiwa 100, kuma sun bayyana cewa suna jiran kammala bincike domin tantance hakikanin adadin mutanen da suka rasa rayukansu da wadanda suka jikkata da kuma sunayensu, duba da cewa abin da ake yi wa mutanen shi ne kisan kare dangi.