Sojojin Sudan Sun Kashe ‘Yan Tawayen Kasar Fiye Da 100 A Babban Birnin Kasar Khartoum

Rundunar Sojin Sudan ta sanar da kashe mayakan Dakarun kai Daukin gaggawa na Rapid Support Forces fiye da 100 Ofishin kakakin rundunar sojin kasar Sudan

Rundunar Sojin Sudan ta sanar da kashe mayakan Dakarun kai Daukin gaggawa na Rapid Support Forces fiye da 100

Ofishin kakakin rundunar sojin kasar Sudan ya sanar da cewa: Sojojin Sudan sun halaka mayakan Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces fiye da 100, a yakin da aka kwashe sama da shekara guda ana yi a Sudan.

Shafin sadarwa na yanar gizo na SUNA na kasar Sudan ya nakalto sanarwa da kakakin rundunar sojin kasar Sudan ya fitar dangane da halin da ake ciki a babban birnin kasar Khartoum, inda ya ce: Tun daga ranar Asabar da ta gabata 13 ga watan Yulin wannan shekara ta 2024, sojojin Sudan sun gudanar da wasu ayyukan tsaro na musamman a babban birnin kasar Khartoum, inda suka yi nasarar halaka ‘yan tawayen kasar na Dakarun kai daukin gaggawa sama da 100 da kuma jikkata wasu da dama, baya ga lalata wasu motocin yakinsu masu yawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments