Ana ci gaba da arangama a yankuna daban-daban na kasar Sudan, tsakanin sojojin kasar da kuma dakarun kai daukin gaggawa
Rahotonni sun bayyana cewa: Arangama tsakanin bangarorin biyu ta fi yin kamari ne a birnin El Fasher, fadar mulkin lardin Darfur ta Arewa, a daidai lokacin da Dakarun kai dauki gaggawa suka kutsa cikin tsakiyar birnin tare da sanar da karbe iko da manyan unguwanni a cikin birnin, baya ga babbar kasuwar birnin da ke kusa da cibiyar rundunar sojin Sudan ta shida wacce ita ce hedikwatar soji mafi girma a yankin Darfur.
Rahotonni sun bayyana cewa: Dakarun kai daukin gaggawan sun kwace iko da fiye da kashi casa’in na yankunan birnin na El Fasher. Sannan a yankin White Nile an gwabza kazamin fada a kusa da birnin Al-Duwaim da yankin Naima da kuma kauyukan birnin Rabak da ke tsakiyar jihar.
Dangane da babban birnin kasar Sudan, Khartoum kuwa, an ci gaba da luguden wuta a garuruwansa uku. Wannan dai yana tabbatar da rahotannin yiwuwar shiga tsakani na kasa da kasa matukar bangarorin biyu da ke fada ba su amince su koma kan teburin tattaunawa ba.