Sama da mayakan kungiyar ta’addanci ta Al-Shabaab 50 ne suka halaka a yankin kudu maso yammacin birnin Mogadishu fadar mulkin kasar somaliya
Tawagar wanzar da zaman lafiya ta Tarayyar Afirka a Somaliya ta sanar a ranar Lahadin da ta gabata cewa; Sama da mayakan kungiyar ta’addanci ta Al-Shabaab 50 ne suka halaka a wani samame da dakarun sojin Somaliya suka kai a garin Bireire da ke kudu maso yammacin Mogadishu fadar mulkin kasar.
Tawagar ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa: “A samamen hadin gwiwa da sojojin kasar Somaliya domin kwato garin Bireire a ranar 1 ga watan Agusta, ya haifar da hasara mai yawa ga ‘yan ta’addar, tare da kashe mayakan Al-Shabaab fiye da 50, wasu kuma sun samu munanan raunuka.”
Tawagar ta ambato wakilin musamman na shugaban hukumar Tarayyar Afirka a Somaliya, Alhaji Ibrahima Deini yana cewa: “Dakarun tawagar da sojojin kasar Somaliya sun kuduri aniyar kwato garin Bireire da sauran yankunan da har yanzu ke karkashin ikon kungiyar Al-Shabaab, domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ga al’ummar Somaliya.”