Sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suna ci gaba da aikata laifin kisan kiyashi a Zirin Gaza na Falasdinu
Sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya suna ci gaba da aikata laifin kisan kiyashi a Zirin Gaza, a rana ta 228 a jere, ta hanyar kai hare-hare da dama ta sama da kuma harba makaman roka kan gidajen jama’a, a yayin da suke aiwatar da kisan kiyashi kan fararen hula, a daidai lokacin da ake cikin wani mummunan yanayi na jin kai sakamakon tsanantan hare-haren wuce gona da iri da killace yankin Gaza da haka ya tilastawa mutane fiye da kashi 95% na al’ummar yankin.
Kamfofin yada labaran Falasdinawa sun bayyana cewa: A safiyar yau talata, jiragen saman yakin sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya suka ci gaba da kai hare-hare da bama-bamai a sassa daban-daban na Zirin Gaza, inda suke kai hare-haren wuce gona da iri kan gidaje, wuraren tarukan ‘yan gudun hijira, da kan tituna, inda suke janyo shahadar Falasdinawa tare da jikkatan wasu masu yawa musamman a birnin Rafah, Jabalia da sauran sassan Arewacin Gaza.