AU Ta Mika Sakon Ta’aziyya Ga Iran

Kungiyar tarayyar Afrika ta mika sakon ta’aziyyarta ga Iran, game da rasuwar shugaban kasar Ibrahim Ra’isi da kuma mukarabansa sakamakon hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu. A cikin wata sanarwa Shugaban kwamitin kungiyar, Moussa Faki Mahamat, ya bayyana matukar kaduwa da bakin ciki da labarin rasuwar Shugaban Kasa Seyeed Ibrahim Raïssi da Ministan Harkokin Waje, […]
Ana Ci Gaba Da Goyan Bayan ICC, Kan Neman Izinin Kama Netanyahu

Al’ummar duniya na ci gaba da bayyana goyon bayansu ga kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) bayan da mai gabatar da kara na kotun, Karim Khan, ya nemi izinin bayar da sammacin kame shugabannin Isra’ila kan kisan kiyashin da ake yi a Gaza duk da adawar da Amurka ta yi kan batun. […]
Nijar Ta Mika Ta’aziyyarta Ga Iran, Game Da Rasuwar Ra’isi

Shugaban Majalisar Tsaron kasa ta Nijar, Birgediya Janar Abdourrahmane Tiani ya gabatar, ya jajantawa gwamnati da kuma al’ummar Iran bayan rasuwar shugaba Ebrahim Ra’isi. Bismillahir Rahmanir Rahim lnna Lillahi wa lnna alayhi Rajiou’n “A cikin bakin ciki da kaduwa ne na samu labarin a ranar 19 ga Mayu, 2024, na Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran, […]
Miliyoyin Iraniyawa Ne Suka Halarci Jana’izar Shugaba Raeisi, Da Mukarabansa

A Iran, miliyoyin mutane ne suka halarci jana’izar shugaban kasar Iran Ebrahim Raeisi da mukarabansa da suka yi shahada a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a arewa maso yammacin kasar. An fara bikin jana’izar ne a safiyar yau Talata a yankin Tabriz, inda aka samu dimbin jama’a galibi sanye da bakaken tufafi, suna […]
Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ta Kore Hannunta A Hatsarin Shugaban Kasar Iran

Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kore hannunta a hatsarin jirgin saman shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi Rahotonni sun bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi gaggawar kore hannunta a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu na shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi da mukarrabansa, tun kafin Iran ta sanar da tabbacin mutuwarsu a […]
Mai Shigar Da Kara A Kotun Kasa Da Kasa Ya Bukaci Fitar Da Sammacin Kama Benjamin Netanyahu

Mai shigar da kara a kotun da ke hukunta manyan laifuka a duniuya da ke birnin Hague ta ICC ya nema fitar da sammacin kama fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu Mai shigar da kara na kotun da ke hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, Karim Khan ya bukaci kotun ta kasa da […]
Sojojin Mamaya Suna Ci Gaba Da Aiwatar Da Kisan Kiyashi Kan Al’ummar Falasdinu

Sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suna ci gaba da aikata laifin kisan kiyashi a Zirin Gaza na Falasdinu Sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya suna ci gaba da aikata laifin kisan kiyashi a Zirin Gaza, a rana ta 228 a jere, ta hanyar kai hare-hare da dama ta sama da kuma harba makaman roka kan gidajen jama’a, […]
Kwamitin Tsaron MDD Ya Yi Shiru Na Minti Guda Domin Girmama Shugaba Ibrahim Raisi

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi shiru na minti daya domin girmamawa da kuma alhini na rasuwar shugaban kasar Iran marigayi Ibrahim Raisi, kamar yadda jakadan kasar Mozambique a MDD Pedro Comissario Afonso, wanda ke jagorantar majalisar a wannan watan ya bayyana. Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, Wakilan Kwamitin Sulhu na […]
Iran ta sanar da sabon ministan harkokin waje na rikon kwarya

Jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran Sayyed Ali Khamenei ya fitar da wata sanarwa inda ya bayyana cewa, mataimakin shugaban kasar Mohammad Mokhber ne zai zama shugaban kasar na wucin gadi, kamar yadda dokar kundin tsarin mulkin kasar ta tanada., inda ya yi kira gare shi da shugabannin ma’aikatun shari’a da na majalisar dokoki […]
Iran za ta gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 28 ga watan Yuni

Shugabannin sassa uku na gwamnatin Iran sun amince da ranar da za a gudanar da zaben shugaban kasa cikin gaggawa a kasar, kwana guda bayan da aka tabbatar da rasuwar shugaba Ibrahim Raeisi a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu da ya yi a arewa maso yammacin kasar. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran […]
Hamas ta yi tsokaci kan kalaman mai shigar da kara na kotun ICC kan batun Gaza

Kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta yi tsokaci kan kalaman mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, Karim Khan, kan kiran da ya yi na a kama tare da tsare Firaministan gwamnatin yahudawan Sahyudawa Benjamin Netanyahu, da kuma ministan yaki Yoav Galant, bayan shudewar watanni 7 suna aikata kisan kare […]