Search
Close this search box.

 Sojojin Kasar Yemen Tare Da “Yan Gwagwarmayar Kasar Iraki Sun Kai Farmakin Hadin Gwiwa Akan Manufofin HKI

A jiya Asabar en dai kakakin sojan kasar Yemen Janar Yahya Sarir’ ya sanar da cewa sun kai harin hadin gwiwa da mayakan Iraki akan

A jiya Asabar en dai kakakin sojan kasar Yemen Janar Yahya Sarir’ ya sanar da cewa sun kai harin hadin gwiwa da mayakan Iraki akan tashar jiragen ruwa ta garin Hiafa,dake gabar ruwan tekn Midtreniya.

Sanarwar ta kuma kara da cewa; harin na hadin gwiwa an yi shi ne ta hanayar harba jirage marasa matuki, an kuma kai shi ne akan jiragen ruwa 5.

Wannan dai shi ne karo na biyu da sojojin Yemen, tare da hadin gwiwar ‘yan gwagwarmayar kasar Iraki su ka kai hari akan manufofin HKI.

Kakakin sojan na kasar Yemen ya kuma kara da cewa; Za su cigaba da kai harin hadin gwiwa irin wannan tare da ‘yan gwgawarmayar Iraki, a cigaba da kare al’ummar Falasdinu.

Tun da HKI ta bude yaki akan Gaza ne, sojojin kasar Yemen su ka shiga cikin sahun masu taya Falasdinawa fada, ta hanar kai wa jiragen ruwa masu zuwa can, hare-hare a mashigar ruwan Babul-Mandab.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments