Sojojin Isra’ila Sun Kutse Cikin Siriya Har Sau 1,068

Kungiyar SOHR mai kula da al-amuran kare hakkin bil’adama a kasar Siriya ta bada sanarwan cewa: Tun bayan faduwar gwamnatin shugaba Bashar Assad na kasar

Kungiyar SOHR mai kula da al-amuran kare hakkin bil’adama a kasar Siriya ta bada sanarwan cewa: Tun bayan faduwar gwamnatin shugaba Bashar Assad na kasar Siriya, sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun kutsa a cikin kasar har sau 1,068.

Tashar talabijan ta Presstv na kasar Iran ta nakalto, kungiyar wacce take da mazauni a kasar Birtaniya tana cewa, daga faduwar shugaban Bashar Al-Asad a cikin watan Decemban shekara ta 2024 ya zuwa watan Satumban da muke ciki, sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun kutsa a cikin kasar Siriya har  fiye da 1000.

Kungiyar ta ce, kutsawar sojojin sun hada da bincike a cikin gidajen mutane da wurare, kama ‘yan kasar ta siriya, da share filaye da gudanar da gine-gine domin samar da sansanonin sojoji.

Daga karshe, kungiyar ta tabbatar da cewa, tun bayan faduwar gwamnatin Bashar Al-asad sojojin mamayar Isra’ila suna cikin Siriya suna kuma kara mamaye kasar. A cikin shekara ta 2025 kadai sojojin yahudawan sahayoniyya sun katsu cikin kasar ta Siriya har sau 460.

A shekara ta 2026 da muke ciki sojojin Isra’ila sun kutsa cikin kasar Siriya har sau 78 , a wasu lokuta har da kai hare hare kan tashar jiragen sama na Idlib da kuma wasu wurare har guda 6.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted